in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi tir da hari kan hukumar zaben Libya
2018-05-03 09:23:09 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi tir da harin ta'addancin da aka kai wa hedkwatar hukumar zaben Libya dake Tripoli, babban birnin kasar.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ya ruwaito Antonio Guterres, na jajantawa wadanda harin ya rutsa da su da kuma iyalansu.

Sakatare Janar din ya kuma jadadda kudurin MDD na aiwatar da jerin manufofin cimma zaman lafiya a kasar, yana mai yabawa tare da godewa manzonsa na musammam dake kasar, Ghassan Salame bisa kokarin da yake yi game da manufofin.

A watan Satumban bara ne manzon na musammam ya gabatar da wasu jerin manufofin da za su kawo karshen rikicin siyasar kasar, wadanda suka kunshi gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa kafin karshen bana.

Harin na jiya Laraba da ya yi sanadin rayuka a kalla 14, ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD, da hadin gwiwar shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar dake aiki a kasar, ke shirin gudanar da zabukan 'yan majalisa da shugaban kasa.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China