in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sudan za su shiga yaki da 'yan tawayen Houthi a Yemen
2018-05-03 09:17:19 cri

Karamin ministan tsaron kasar Sudan Ali Mohamed Salem ya bayyana cewa, kasarsa na duba yiwuwar shigar da sojojinta cikin kawancen kasashen Larabawa dake yakar 'yan tawayen Houthi, da ma goyon bayan gwamnatin kasar ta Yemen da duniya ta amince da ita.

Ministan wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ya ce yanzu haka suna nazartar fa'ida da rashin fa'idar shigar sojojin kasar cikin wannan kawance. Kuma nan ba da dadewa ba za a bayyana shawarar da kasar ta yanke wadda za ta dace da muradun kasar, da ma al'amuranta na tsaro da zaman lafiya. A hannun guda kuma Sudan ta ba da tabbaci game da kudurinta na shiga a dama da ita a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Ko da yake kungiyar nan dake rajin kawo canji a kasar mai suna Alliance for Change, wadda ta kunshi 'yan majalisar dokokin kasar masu zaman kansu, ta bayar da wata sanarwa a baya-bayan, inda ta bukaci a janye sojojin kasar daga kasar Yemen.

Tun a ranar 26 ga watan Maris din shekarar 2015 ne dai kasar Sudan ta shiga kawance kasashen Larabawa da ke yaki da 'yan tawayen Houthi a Yemen wadda Saudiya ta ke jagoranta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China