in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Dominica ya dace da manufofin sassan biyu
2018-05-02 20:27:30 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce sharadi daya tilo na kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da jamhuriyar Dominica, shi ne amincewa da kasar Sin daya tak a duniya.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin da aka bukaci ta yi tsokaci, game da zargin da mahukuntan yankin Taiwan suka yi, cewa babban yankin kasar Sin ya baiwa janhuriyar Dominica tarin kudade, domin ta amince ta katse dangantaka da Taiwan.

Hua ta ce Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin ita ce daya kadai ke wakiltar al'ummar Sinawa tsakankanin sauran kasashen duniya baki daya. Kaza lika yankin Taiwan bangare ne na Sin wanda ba za a iya balle shi ba.

A daya hannun kuma, matakin da jamhuriyar Dominica ta dauka na katse dangantaka da Taiwan, tare da kulla alaka da Sin, ya dace da ka'idoji da dokokin kasa da kasa da ma huldar diflomasiyyar duniya. Don haka a cewar jami'ar, kulla dangantaka tsakanin Sin da Dominica, ya yi daidai da muradun al'ummun kasashen biyu, yana kuma da ma'ana, da kyakkyawar makoma.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China