in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu Sinawa sun yi aiki a ranar ma'aikata ta kasa da kasa
2018-05-02 10:54:30 cri

Jiya Litinin 1 ga wata, rana ce ta ma'aikata ta duniya, domin murnar wannan rana, yawancin Sinawa sun huta a gida ko sun fita waje yawon shakatawa, amma wasu sun ci gaba da gudanar da sana'o'i daban daban.

Huang Xianbo, jagoran aikin fasaha a wani kamfani mai zaman kansa na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, tun bayan da ya fara aiki a kamfanin shekaru sama da 20 da suka gabata, ya dukufa kan aikin kirkire kirkire, kuma ya samu babban sakamako bayan kokarin da ya yi tare da abokan aikinsa, misali kamfaninsa ya samar da kayayyakin da ake bukata wajen kera jiragen sama da na'urorin zirga-zirgar sararin samaniya, Huang Xianbo ya gamsu da wannan sakamako saboda kokarinsu ya ciyar da fasahohin zirga-zirgar sararin samaniya gaba matuka, ya gaya mana cewa, yana kaunar aikin da yake a ofishin yin nazarin fasahohin zamani, yana mai cewa, "Ina jin dadin aikina a ofishin yin nazari, saboda ina gudanar da muhimman aikin nazarin kimiyya da fasaha, ina ganin cewa, aikin da muke yi yana da ma'ana sosai, kana ina son samarwa matasa masu aikin yin nazarin kimiyya da fasaha damammaki, ta yadda za su samu nasara a hanyar yin kirkire kirkire, haka kuma kamfaninmu shi ma zai habaka sannu a hankali."

Tekun Lingding yana hanyar ruwan kogin Zhujiang dake lardin Guangdong, an gina babban kadarkon dake hada yankin Hongkong da birnin Zhuhai na lardin Guangdong da kuma yankin Macau a kan tekun, a cikin ruwan tekun, ana samun dabbar dolphin mai daraja da yawa, Wen Hua ta taba karatu a Birtaniya, tun can da, ta mai da hankali matuka kan dabbar, yanzu tana aiki a sashen kiyaye muhalli na hukumar kula da babban kadarkon Zhujiang-Hongkong-Macau, aikinta na yau da kullum shi ne tsara matakan kiyaye ruwan tekun da dabbar dolphin ke rayuwa, ta bayyana cewa, "Launin jikin dabbar Dolphin yana sauyawa yayin da take girma, inda ka ga launinta ya sauya zuwa fari, to, ta girma ke nan, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, muna kokarin kaucewa kazantar ruwan tekun yayin da ake gina kadarkon, nan gaba za mu ci gaba da kokarin kiyaye muhallin, ta yadda za a samar musu da ingantaccen muhalli."

Yayin da ake bikin 'yan kwadagon kasa da kasa a nan kasar Sin, masu bude ido da dama sun je jihar Xizang mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya haifar da matsalar cunkuson motoci.

Pakhu, 'dan sandan kula da zirga-zirgar ababan hawa ne na birnin Lhasa, hedkwatar jihar, kawo yanzu ya yi aiki na tsawon shekaru 35, ya gaya mana cewa, "A ranar 1 ga watan Mayun ko wace shekara, na saba yin aiki a kan hanya, saboda nauyi dake kanmu mu tabbatar da tsaron jama'a dake bin titi, duk da cewa, na gaji saboda na tsaya kan hanya a duk tsawon rana, amma na yi farin ciki."

A birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin kuwa, an shirya wata babbar gasar nuna gwanintar aiki, Li Peizhi, mai aikin gini wanda ya shiga gasar ya bayyana cewa, "A ko da yaushe muna mai da hankali kan ingancin aikinmu, kuma mun saba da sadaukar da ranmu kan aiki, dalilin da ya sa haka shi ne domin muna kaunar aikinmu muna kuma kaunar kasarmu."

A daren jiya, 1 ga wata, babbar kungiyar 'yan kwadagon kasar Sin da babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG sun shirya wani shiri na musamman mai taken "Burin kasar Sin da alfaharin 'yan kwadago" cikin hadin gwiwa domin murnar ranar 'yan kwadagon kasa da kasa, inda aka tsara shirin a wurare biyu wato birnin Beijing da kuma birnin Changchun na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar, a cikin shirin da aka tsara, an isar da gaisuwa da fatan alheri ga daukacin 'yan kwadagon fadin kasar ta Sin, shirin da ya samu halartar 'yan kwadagon da suka samu lambobin yabon 'yan kwadagon kasar Sin da wakilan fitattun 'yan kwadago daga sassan sana'o'i daban daban.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China