in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Afghanistan
2018-05-02 09:41:44 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa a jiya, inda da kakkausar murya,ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai a Afghanistan a ran 30 ga watan Afrilu.

Sanarwar ta ce, mambobin kwamitin sun nuna juyayi ga gwamnatin kasar da ma iyalan mamata tare kuma da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.

Ban da wannan kuma, sanarwar ta jaddada cewa, tilas ne a gurfanar da wadanda suka aikata laifin, da wadanda suka tsara, da wadanda suka jagoranta, har ma da masu goyon bayan ayyukan ta'addanci a gaban kuliya. Haka kuma kamata ya yi kasashen duniya su hada kai da gwamnatin Afghanistan da sauran bangarori masu ruwa da tsaki bisa dokar kasa da kasa da kudurorin kwamitin sulhu.

Haka zalika, kwamitin ya jaddada cewa, ta'addanci babban kalubale ne ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, a don haka ya kamata kasashen duniya su hada kai don kawar da mummunan tasirin da ayyukan ta'addanci suke kawowa zaman lafiya da tsaron kasashen duniya.

Bayanai na nuna cewa, a ran 30 ga wata Afrilu ne, aka kai harin bam a Kabul da Kandahar dake kudancin kasar. Alkaluman kididdigar kwamitin sulhu sun nuna cewa, hare-haren da aka kai a wannan karo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 41 yayin da wasu 45 kuma suka jikkata. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China