in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta dage aiwatar da karin harajin ta ga kasashen EU da Canada da Mexico
2018-05-01 16:30:58 cri
Fadar White House ta Amurka, ta sanar da dage fara aiwatar da sabon haraji kan albarkatun karafa da gangar ruwa, kan kasashen dake kungiyar tarayyar Turai ta EU, da kasashen Canada, da Mexico, ya zuwa ranar 1 ga watan Yuni dake tafe. Amurka ta dauki wannan mataki ne dai domin baiwa kasashen damar tattaunawa da ita, domin cimma wata matsaya ta cinikayya wadda kowa zai amince da ita.

Kafin hakan, Amurka ta riga da dage wancan haraji kan kasashen Argentina, da Australia da Brazil, bayan da ta cimma matsaya da su, game da tsarin cinikayyar karafa da gangar ruwa. Fadar White House ta ce nan gaba kadan za a kammala yarjejeniya da wadannan kasashe.

Duk dai da suka da wannan manufa ta karin haraji ta sha daga sassan 'yan kasuwa a Amurka, da ma sauran abokan huldar cinikayyar kasar na ketare, shugaba Trump ya sanya hannu kan dokar karin harajin kaso 25 bisa dari kan hajojin karafa, da kuma kaso 10 bisa dari na kayan gangar ruwa da ake shigarwa Amurka, dokar da ta fara aiki tun daga ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata.

Fadar White House ta ce Amurka, ta amince da dagawa kasashe mambobin EU da Argentina, da Australia, da Brazil, da Canada, da Mexico da Koriya ta kudu kafa na dan lokaci.

Amurka dai na amfani da wata tsohuwar doka ne mai nasaba da tsaron kasa, wajen aiwatar da manufar karin harajin na wannan karo, matakin da ya sha suka daga sassan 'yan kasuwar kasar, da abokan huldar ta na ketare.

A makon da ya gabata ma shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun ziyarci birnin Washington na Amurka, domin tattauna batutuwan da suka jibanci cinikayyar kasa da kasa tsakanin su da Amurka. To sai dai kuma har karshen ziyarar ta su, ba su kai ga cimma nasarar warware wannan takaddama ta cinikayya ba.

Da yake tsokaci game da wannan kalubale, wani masanin harkokin tattalin arziki a cibiyar kasa da kasa ta Peterson Mr. Chad Bown, ya ce matakin kashin kai na kara haraji da Amurka ta dauka, zai haddasa hasara ga dukkanin sassan da take cinikayya da su har ma da ita kan ta Amurka, tare da gurgunta tsarin kasuwanci da ake bi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China