Da yake karin haske game da hakan, shugaban cibiyar Lassaad Boujebal, ya ce bude wannan cibiya zai samar wa kasar Tunisia damar shigo da jari, wanda ya kai kusan dalar Amurka miliyan 20.47, tare da guraben ayyukan yi 100, da suka hada da likitoci da masana a fannin harhada magunguna.
Lassaad Boujebal, ya ce cibiyar na kunshe da dakin harhada magunguna na sarrafa maganin cutar daji da ma sauran cututtuka.
A nasa bangare kuwa, firaministan kasar Youssef Chahed, cewa ya yi kasar sa, na fatan biyan bukatun al'ummar ta, game da samar da magunguna na gida da kaso 60 bisa dari nan da shekarar 2020, adadin da zai haura kaso 51 bisa dari da kasar ke da shi a shekarar 2016.
Youssef Chahed ya ce sashen masana'antun harhada magunguna na Tunisia, na fatan samar da kudaden jarin da yawan su zai kai dala biliyan 1.35 nan da shekarar 2020.