in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump zai gana da Kim Jong Un cikin makonni uku ko hudu
2018-04-29 16:39:56 cri
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana a birnin Michigan na Amurkar ranar Asabar cewa, zai gana da takwaransa na Koriya ta Arewa cikin makonni uku ko hudu.

Fadar Amurka ta White House ta sanar a wannan rana cewa,shugaba Trump ya tattauna ta wayar tarho da shugaba Moon Jae-in na Koriya ta kudu da firaministan Japan Shinzo Abe game da ci gaban da aka samu a zirin Koriya.

A tattaunawar da Trump ya yi tare da Moon Jae-in, ya jaddada cewa, za a iya samar da zaman lafiya da kyakkyawar makoma ga Koriya ta arewa muddin an tabbatar da kawar da makaman nukiliyar kasar.

Sai kuma a zantawa ta daban ta wayar tarho da Shinzo Abe na Japan, shugabannin biyu sun nanata bukatar ganin Koriya ta Arewa ta yi watsi da dukkan makamanta na kare dangi, da shirinta na kera makamai masu linzami.

Shugaba Trump ya kuma shaidawa taron manema labarai a Jumma'a cewa, yana da kyakkyawar alaka da shugaba Kim Jong Un na koriya ta arewa, kuma za su sanar da kasar da kuma wurin da za su gana da shugaba Kim. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China