in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani: Kasashen Afirka sun samu gagarumar nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa
2018-04-29 16:24:28 cri
Tsohon shugaban bankin raya Afirka Donald Kaberuka ya ce kasashen nahiyar Afirka sun samu gagarumar nasara wajen rage matsalar cin hanci da rashawa, duk da tafiyar hawainiyar da ake samu wajen yakar matsalar da ta dade tana addabar kasashen nahiyar.

Masanin tattalin arzikin dan kasar Rwanda wanda ya bayyana hakan a gefen taron auna shugabanci na gari na Mo Ibrahim na shekara-shekara da aka gudanar da karshen mako a birnin Kigalin kasar Rwanda, ya ce, kasashen na Afirka sun kara kaimi wajen magance wannan matsala.

Kaberuka ya ce yanzu haka gwamnatocin kasashen Afirka sun kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa, matsalar ta fi kamari a bangaren samar da mai da iskar gas da sassan kula da harkokin kudi na nahiyar, kuma matsalar ta yi matukar tasiri ga nahiyar.

A cewar gidauniyar Mo Ibrahim, nahiyar na asarar kudaden da suka kai sama da dala biliyan 148 a duk shekara, daidai da kaso 50 cikin 100 na kudaden harajin nahiyar, kwatankwacin kaso 25 cikin na GDPn nahiyar baki daya.

Masu shirya taron sun bayyana cewa, a ranar Jumma'a ce aka bude taron gidauniyar Mo Ibrahim na kwanaki uku, taron da ya halartar fitattun shugabannin siyasa da 'yan kasuwar nahiyar, da wakilan kungiyoyin fararen hula, da hukomomin kasa da kasa da na shiyya da manyan abokan huldar Afirka, inda suka tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi nahiyar Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China