in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sashe na 301 na dokar cinikayyar Amurka na kalubalantar tubalin tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa
2018-04-28 16:35:09 cri
Jami'in diflomasiyyar kasar Sin Yu Benlin, ya ce an farfado da yanayin daukar ra'ayi na kashin kai na sashe na 301 na dokar cinikayyar Amurka, wanda a yanzu ke kalubalantar tubalin tsarin cinikayya tsakanin kasa da aka gina bisa ka'idoji.

Yu Benlin, wanda ya bayyana haka yayin da yake gabatar da jawabi ga taron hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO da ya gudana jiya Juma'a, ya bayyana damuwar kasar Sin game da yanke hukunci da Amurka ta yi bisa binciken da ta yi karkashin sashe na 301, inda ta zargi kasar Sin da take hakkokin mallakar fasaha, tare da daukar matakai, ciki har da kakaba karin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar.

Ya bayyana cewa, tun bayan zartar da dokar ta sashe na 301 a 1974, an yi amfani da ita wajen binciken galibin mambobin WTO ciki har da Tarayyar Turai da Japan da Canada da sauransu, inda daga bisani aka tilasta musu bude kawuwanninsu ga kamfanonin Amurka ko kuma a kakaba musu matakan daukar fansa.

Ya yi kira ga dukkan mambobin WTO su tsaya tsayin daka wajen nuna adawa da daukar ra'ayi na kashin kai da matakan cinikayya masu tsauri da Amurka ta bullo da su a baya-bayan nan, domin kare maimaituwar abun da ya faru a baya.

Har ila yau yayin taron, kasashen Rasha da Pakistan sun bayyana damuwa ainun, game da tasirin da matakan na Amurka za su yi ga tsarin cinikayyar duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China