in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar aikin gona ta Amurka: Takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka ta kawo illa ga aikin gona a Amurka
2018-04-28 11:16:19 cri

Wata kungiyar aikin gona ta kasar Amurka ta ba da rahoto a kwanan baya cewa, aikin fitar da kayayyakin noma na Amurka na fuskantar kalubale saboda matakin da Amurka ta dauka na kara kudaden haraji a kan kayayyakin karafa da gorar ruwa da kasar Sin ke shigarwa kasar, wanda ya haifar da takaddamar ciniki tsakanin kasashen biyu. Mataki kuma zai sa farashin kayayyakin gonan kasar ya ragu. Abin da zai tilasta Sin ta shigo da wadannan kayayyakin daga sauran kasashe. Kungiyar ta ce, wannan mataki ya lahanta moriyar manoman Amurka, wato harajin kwastan da za a bugawa manoman Amurka zai karu.

Ban da wannan kuma kungiyar ta yi gargadi cewa, idan gwamnati ta ci gaba da daukar ko habaka irin wannan mataki, Sin za ta mai da martani da iyakacin kokarinta, aikin gonar Amurka zai fuskanci kalubale mai tsanani. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China