in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NATO za ta yi shawarwari da Rasha tare da mai da martani
2018-04-28 10:56:17 cri

An kira wani taron ministocin harkokin waje na kasashe mambobin NATO a jiya Juma'a 27 ga wata a Brussels, inda babban sakataren NATO Jens Stoltenberg ya shedawa manema labarai bayan taron cewa, NATO ta jaddada manufar da take aiwatarwa ta nacewa ga matakin mai da martani da yin shawarwari da Rasha.

A wannan rana a gun taron, ministocin harkokin waje na kasashen mambobin NATO sun tattauna kan dangantakar dake tsakanin kungiyar da Rasha, inda sun nuna damuwa kan tasirin da Rasha ke kawo wa sauran kasashe a fannin diplomasiyya da tsaro. Ministocin sun cimma matsaya daya cewa, NATO za ta ci gaba da daukar matakin mai da martani kan Rasha tare kuma yin shawarwari.

Stoltenberg ya ce, Rasha ta dauki wasu natakai wadanda suka haifar da rikici, kasashen mambobin NATO sun mai da martani cikin hadin kai kan wadannan batutuwa, ciki hadda rikicin Ukraine, babban zaben Amurka, rikicin masu leken asiri tsakanin Birtaniya da Rasha, matsalar Sham da sauransu. Kamata ya yi, NATO za ta ci gaba da daukar matakin da ya fi dacewa don tinkarar wadannan kalubaloli. Ya ce, har kullum NATO ta dukufa kan yin shawarwari da Rasha. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China