in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Arewa da ta Kudu sun fitar da sanarwar Panmunjom
2018-04-28 10:02:58 cri

Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ta gana da takwaransa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un a Panmunjom a jiya Juma'a 27 ga wata, inda suka sa hannu kan sanarwar Panmunjom, tare da sanar da niyyarsu ta kokarin tabbatar da kawar da makaman nukiliya da samar da zaman lafiya a zirin.

Moon Jae-in ya ce, yaki ba zai abku a zirin ba, an bude sabon shafi na zaman lafiya. A nasa bangare kuma, Kim Jong Un ya ce, sun cimma matsaya daya na samar da sabon zamani mai wadata a kan ziri maras yaki bisa niyyarsu da nauyin dake wuyansu gaba daya.

Sanarwar ta tanadi muradin da za a samu cikin hadin gwiwa na kawar da makaman nukiliya a zirin. Bangarorin biyu sun sanar da cewa, domin tabbatar da zaman lafiya mai karko a zirin, za su sa kami ga shawarwari tsakaninsu da Amurka ko kuma kasar Sin.

Ban da wannan kuma, sanarwar ta bayyana cewa, bangarorin biyu za su daina yin gaba da juna don kara tuntubar juna da hadin gwiwa tsakaninsu. Hakazalika, sun kai ga matsaya daya cewa, Moon Jae-in zai kai ziyara a Koriya ta Arewa a lokacin kaka na bana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China