in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu sun yi ganawa a Panmunjom
2018-04-27 12:42:46 cri
Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ya gana da takwaransa na kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un a yau Jumma'a a Panmunjom.

Misalin karfe 9 da rabi bisa agogon wurin, Kim Jong Un ya isa kan iyakar soja dake tsakanin kasarsa da kasar Koriya ta Kudu, sa'an nan ya shiga cikin kasar Koriya ta Kudu, inda ya samun maraba hannun biyu-biyu daga Moon Jae-in, wanda yake jiran sa a wurin. Kuma wannan shi ne karo na farko da babban shugaban kasar Koriya ta Arewa ya shiga cikin kasar Koriya ta Kudu tun bayan yakin Koriya.

Kasar Koriya ta Kudu ta shirya wani bikin maraba da zuwan Kim Jong Un, da kuma bikin duba faretin soja. Kuma wannan shi karo na farko da shugaban kasar Koriya ta Arewa ya duba ayyukan kungiyar sojoji masu nuna girmamawa ta kasar Koriya ta Kudu

Sa'an nan kuma, misalin karfe 10 da kwata, shugabannin biyu sun fara shawarwarin tsakaninsu a Gidan Zaman Lafiya dake kasar Koriya ta Kudu.

Bisa bayanin da fadar shugaban kasa ta Koriya ta Kudu ta fidda a jiya Alhamis, an ce, ganawar shugabannin biyu za ta mai da hankali kan kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da kuma shimfida zaman lafiya na din din din a zirin gaba daya. Sai dai batu da ka iya zama mai wahala gare su shi ne, kulla wata yarjejeniya kan batun nukiliya. Haka zalika, wannan ita ce ganawa karo na uku a tsakanin shugabannin kolin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China