in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar kasuwanci ta Sin ta mayar da martani ga batun kayyade zuba jari da mai yiwuwa kasar Amurka za ta zartas kan kasar Sin
2018-04-27 11:03:11 cri

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, kasar Sin ta shirya tsaf don tinkarar manufar Amurka ta shirin aiwatar da kayyade yawan jarin da Sin za ta iya zubawa a kasar Amurka.

Gao Feng ya ce Sin za ta tunkari wannan kalubale bisa ka'idojin da ta amince da su.

Wani jami'in ma'aikatar kudi ta kasar Amurka ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Amurka tana yin nazari kan yiwuwar aiwatar da dokokin kare hakki cikin gaggawa, kan zuba jari da kasar Sin ta yi, inda za a kayyade yawan jarin da kasar Sin din za ta iya zubawa a kasar Amurka, da hana Sin samun wasu muhimman fasahohi na musamman. Game da wannan, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Gao Feng ya jaddada a gun wani taron manema labaru da ya gudana a nan birnin Beijing cewa, Sin ta ki amincewa da duk wani irin ra'ayin bada kariya ga cinikayya. Ya ce,

"A shekarun baya baya nan, kamfanonin kasar Sin sun zuba jari a kasar Amurka, wanda ya samar da gudummawa ga kasar Amurkan wajen kara samar da aikin yi, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Ana fatan kasar Amurka za ta maida hankali ga gudanar da ayyukan da suka dace, da bunkasuwar tattalin arzikinta da na duniya baki daya, ta yadda hakan zai taimaka wajen kiyaye bunkasuwar tattalin arzikinta, da na duniya baki daya a dogon lokaci."

Gao Feng ya jaddada cewa, game da ra'ayin kasar Amurka, kasar Sin ta ji abin da kasar ta fada, kuma za ta mai da hankali kan matakan da za ta dauka. Sin ta riga ta shirya sosai bisa ka'idojin da ta amince da su dangane da batun.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2016, kasar Sin ta zuba jari ga kasar Amurka kai tsaye da dala biliyan 109 a fannonin bada hidima, da kera kayayyaki, da gine-gine, da sadarwa da dai sauransu. An gudanar da ayyukan da Sin ta zuba jari a jihohi 46 na kasar Amurka, wadanda suka samar da guraben aikin yi fiye da dubu 141 ga kasar Amurka.

A nata bangare, kungiyar tarayyar Turai ta EU ta ce, za ta nuna goyon baya ga rokon da kasar Sin ta gabatarwa kungiyar WTO, don tinkarar mataki mai lamba 232 da kasar Amurka ta dauka kan kayayyakin karafa da goran ruwa da ake shigarwa Amurka daga kasar Sin da kungiyar EU da sauran kasashe.

Gao Feng ya bayyana cewa, a ranar 16 ga wannan wata, kungiyar EU ta mika wasika ga kasar Amurka, inda ta bukace ta da ta shiga shawarwari tare da kungiyar, kan mataki mai lamba 232, bisa yarjejeniyar matakan tabbatar da ciniki. EU ta ce, ko da yake kasar Amurka ta maida mataki mai lamba 232 a matsayin matakin kiyaye tsaron kasa, amma hakika matakin na bada kariya ga cinikinta ne. Wannan ra'ayi ya yi daidai da na kasar Sin. Gao Feng ya yi nuni da cewa,

"Ya zuwa yanzu, ban da kungiyar EU, kasar Rasha, da Indiya da Turkiya su ma sun gabatar da bukatun yin shawarwarin iri daya. A ranar 19 ga watan Afrilu, kungiyar EU ta sake mika wasika ga kasar Amurka, inda take neman halartar shawarwari da ake gudanar tsakanin bangarorin Amurka da Sin, a matsayin wani bangare na uku. Ban da kungiyar EU, yankin Hongkong na kasar Sin, kasar Rasha, Indiya, Thailand su ma su gabatar da irin wannan bukata ta shiga shawarwarin."

Gao Feng ya jaddada cewa, matakin da kasar Amurka ta dauka ya saba wa ka'idojin kungiyar WTO, zai kuma kawo illa ga moriyar membobin kungiyar WTO ciki har da kasar Sin. Kasar Sin za ta yi kokari tare da membobin kungiyar WTO da abin ya shafa don tabbatar da hakkinsu.

Ban da wannan kuma, Sin tana shirya gabatar da takardar fadada shigar da kayayyaki don sa kaimi ga cimma daidaito kan cinikin dake tsakaninta da kasashen waje. Gao Feng ya yi bayanin cewa,

"A halin yanzu, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin tana nazari kan manufofi da matakan fadada shigar da kayayyaki daga kasashen waje, tare da hukumomin da abin ya shafa. Za a rage yawan harajin kayayyakin da aka shigowa da su a dukkan fannoni, da rage harajin kwastam na motoci da wasu kayayyakin yau da kullum, da kara shigar da kayayyakin musamman bisa bukatun jama'ar kasar, da gabatar da matakan kawo sauki a fannin ciniki, da kuma shirya gudanar da taron koli na shigar da kayayyaki na kasa da kasa karo na farko a kasar Sin." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China