in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MOC: kasar Sin na kokarin bullo da manufofin kara shigo da kayayyaki
2018-04-26 20:40:35 cri
A wani labarin kuma, kakakin ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin Gao Feng, ya bayyana cewa, kasar Sin tana shirin bullo da wasu manufofi da matakai da su kai ga fadada shigo da kayayyaki cikin kasar a wani mataki na ganin bikin baje kolin shigowa da kuma fitar da kayayyaki na kasa da kasa na kasar Sin (CIIE) da zai gudana a karshen wannan shekara ya kai ga nasara.

Kakakin ya kuma bayyana cewa, ana sa ran kasashe 61 za su halarci bikin da ake shirya gudanarwa a birnin Shanghai na kasar Sin a watan Nuwamba mai zuwa, bikin da ake sa ran zai karade filin da ya kai murabbin mita 175,000.

Ya ce, ya zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, kamfanoni 1,022 ne suka nuna sha'awarsu ta halartar bikin, kuma kusan 100 daga cikinsu na daga cikin manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya. Kana kashi 34 cikin 100 na wadannan kamfanoni sun fito ne daga kasashe masu tasowa, kaso 34 bisa 100 kuma daga kasashen dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", sai kuma kaso 10 cikin 100 da suka fito daga kasashe masu karancin ci gaba. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China