Gao Feng wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce sashi na 232 da 301 na dokar kasar Amurka ya sabawa tsarin cinikayyar kasa da kasa, kuma daukacin mambobin WTO ba sa goyon bayan matakan sashi na 232 na dokar ta Amurka, wadanda suka kai ga sanya haraji kan yadda ake shigo da karafa da gorar ruwa cikin kasar.
Jami'in na kasar Sin ya ce, mambobin WTO da suka hada da EU da kasashen Rasha da Indiya za su bi sahun kasar Sin wajen yin tattaunawa karkashin tsarin daidaita takadddamar WTO da Amurka game da wannan batu. (Ibrahim Yaya)