Ma'aikatar harkokin wajen kasar Libiya ta shirya taro na 3, game da tattauna kan batun kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba. Taron da ya gudana gaban manyan jami'ai, ciki hadda wakilan hukumomin kasa da kasa, da jakadun kasashen ketare dake aiki a Libiyan, tare kuma da wakilan shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron, ta bayyana cewa mahalartansa, sun saurari sassan da kasar Libiya ke baiwa fifiko game da bukatar tallafin kasa da kasa a fannin shige da fice. Sun kuma nazarci dabarun da ake amfani da su a yanzu haka, da yadda za a gwama su da manufofin da ake aiwatarwa a yanzu, duka dai da nufin shawo kan kalubalen da kasar ke ci gaba da fuskanta.
Sanarwar ta kara da cewa, wasu daga muhimman kudurori da aka zayyana, sun hada da tsarin ci gaban kasar, da dabarun dakile kwararar 'yan ci rani da safarar bil Adama.
Har wa yau an yi musayar yawu game da bukatun manyan biranen Libiya, da bukatar shigar masu zuba jari a fannin inganta noma a kudancin kasar, a matsayin hanyoyin magance kalubalen 'yan ci rani da kasar ke fuskanta.
Ma'aikatar kwadago ta kasar Libiya na kokarin magance wasu daga wadannan kalubale, inda take maida hankali sosai ga samar da damammaki, da dabarun samarwa jama'a sana'o'i a cikin kasar.(Saminu)