in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron kolin kiyaye zaman lafiya a MDD
2018-04-26 10:45:10 cri

An shirya taron kolin kiyaye zaman lafiya tsakanin ranekun 24 da 25 ga wata, a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka, inda aka tattauna kan batutuwan dake shafar magance aukuwar rikici, da shiga tsakani, da yin shawarwari, da kuma daidaita matsaloli ta hanyar diplomasiya.

Yayin taro na tsawon kwanaki biyu na manyan jami'ai da aka kira domin zakulo hanyoyin wanzarwa da kuma kiyaye zaman lafiya, wasu shugabannin kasashe da na gwamnatoci, da wakilan kungiyoyin jama'a da na kungiyoyi masu zaman kansu, sun yi tattaunawa kan batutuwan dake shafar wanzar da zaman lafiya da kuma kiyaye shi a fadin duniya; Misali akwai batun yadda za a daidaita matsalolin da za su haifar da rikici, da daga matsayin kiyaye zaman lafiya na MDD, da kara zuba jari kan aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, da kara karfafa huldar abokantaka dake tsakanin kasa da kasa, da samar da karin damammaki ga mata da matasa, domin su taka rawa a cikin aikin magance aukuwar rikici, da kuma wanzar da zaman lafiya da sauransu.

A cikin jawabin da ya gabatar a gun bikin bude taron, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru kusan 30 da suka gabata, da dama daga kasashe a fadin duniya suna fama da matsalolin rikice-rikice, a don haka yana fatan al'ummar kasashen duniya su dauki matakai domin samar da taimako gare su. Ya ci gaba da cewa, kafin shekaru biyu da suka gabata, babban taron MDD da kwamitin sulhun MDD sun zartas da kudurori guda biyu, inda aka yi alkawari cewa, za a yi kokari matuka domin kiyaye zaman lafiya a fadin kasashen duniya, yanzu haka yana sa ran cewa, taron kolin zai sa kaimi ga aiwatar da kuduran da suka shafi hakan, yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, daukacin kasashen duniya suna fuskantar kalubale iri daya, shi ya sa wajibi ne su kara karfafa huldar abokantaka dake tsakaninsu; misali gwamnatocin kasashe daban daban, da MDD, da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya shiyya, da hukumomin kudi na kasa da kasa, da kungiyoyin jama'a dake kunshe da mata da matasa da sauransu. Kamata ya yi sassa daban daban su kara mai da hankali kan hakan. Haka kuma su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su magance aukuwar rikici da kuma daidaita rikici, tare kuma da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a fadin duniya."

Shugaban babban taron MDD karo na 72 Miroslav Lajcak, ya jagoranci taron kolin, inda ya bayyana cewa, MDD tana bukatar wani tunani na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, ba ma kawai don samar da taimako ga kasashen dake fama da rikice-rikice ba, domin ya fi muhimmanci a kara sanya kokari na magance aukuwar rikici, a cewarsa: "Ya kamata mu kara mai da hankali kan aikin magance aukuwar rikici, don haka muna bukatar kara azama kan aikin sulhuntawa, da shiga tsakanin shiyya shiyya, da kuma kasa da kasa. A sa'i daya kuma, yana da muhimmanci a kara mai da hankali kan aikin warware matsalolin da suke haifar da rikici."

Jiya Laraba 25 ga wata, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu, shi ma ya gabatar da wani jawabi a madadin mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, inda ya yi nuni da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, majalisar dinkin duniya, ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da taimako ga kasashen dake fama da rikice-rikice, kuma ta ba da babbar gudumowa ga kasashen yayin da suke kokarin samun dauwamammen ci gaba. Ya ce kasar Sin tana fatan kokari tare da sauran kasashe, domin tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya, yana mai cewa, "A nan bari in gabatar da wasu ra'ayoyin kasar Sin game da wanzar da zaman lafiya a fadin duniya. Na farko, nuna biyayya ga ka'idojin MDD da na huldar kasa da kasa. Na biyu, kara mai da hankali kan ci gaban kasa da tsaron kasa tare. Na uku, kara karfafa ikon MDD wajen shiga tsakani. Ban da haka kuma, kasar Sin tana nacewa ga kiyaye tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin MDD, tare kuma da goyon bayan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Kasar Sin tana kuma fatan more sakamakon da ta samu tare da sauran kasashen duniya, haka kuma tana son samun ci gaba da wadata tare da su, ta yadda za a kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China