in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar Sin dake Hongkong ta bukaci EU da ta dakatar da tsoma baki kan harkokin yankin da na cikin gida na Sin
2018-04-25 13:26:42 cri
Kakakin hukumar musamman ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin Hongkong, ya mayar da martani ga rahoton shekara-shekara na yankin Hongkong na shekarar 2017 da kungiyar EU ta gabatar a ranar 24 ga wata, yana mai bukatar kungiyar ta EU da ta dakatar da zargin manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu, da kuma dokokin yankin Hongkong. Kana ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin yankin Hongkong da harkokin cikin gida na kasar Sin.

Kakakin ya yi nuni a wannan rana cewa, rahoton ba shi da tushe, yana kuma kunshe da nuna bambanci ga yankin Hongkong, ya kuma bayar da ra'ayoyi maras dacewa ga harkokin yankin Hongkong. Don haka dai kasar Sin ta yi watsi da wannan rahoto. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China