Gwamnatin kasar ta bayyana ta cikin wata sanarwa cewa, korar masu neman mafakar ba zabi ba ne a wannan gaba, musamman game da 'yan ci ranin kasashen Uganda ko Rwanda dake cikin yankunan Isra'ilan.
Alkaluman da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar sun nuna cewa, akwai masu neman mafaka kusan 42,000 'yan asalin kasashen Afirka dake zaune a kasar, wadanda da daman su ke zaune a yankunan marasa galihu dake kudancin birnin Tel Aviv.(Saminu Alhassan)