in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano sama da gawawwakin mutane 200 a wani kabarin bai daya a Rwanda
2018-04-25 11:41:53 cri

Kungiyar wandada suka tsira ta Ibuka ta kasar Rwanda, ta ce sama da gawawwaki 200 aka tonu daga wani kabari na bai daya, na wadanda kisan kiyashin kasar na 1994 ya rutsa da su.

Shugaban kungiyar Theogene Kabagambire, ya ce an ajiye gawawwakin da aka tono daga kabarin mai zurfin mita 30 na yankin Rusororo na Lardin Gasabo a ofisoshin lardin, inda ake jiran yi musu jana'izar da ta dace.

Ya kara da cewa, akwai wasu kaburbura 3 na bai daya da ba a kai ga tonowa ba a wannan yankin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China