in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar wakilan kasar Rwanda ta amince da yarjejeniyar samar da yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka
2018-04-25 11:40:30 cri

Majalissar wakilan kasar Rwanda ta amince da yarjejeniyar samar da yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka ko AfCFTA a takaice. Yayin zaman ta na jiya Talata, majalissar ya amince da wani kuduri da gagarumin rinjaye, wanda ke kunshe da amincewa da wannan yarjejeniya ta AfCFTA.

Kaza lika kudurin ya amince da wasu tsare tsare, da dokokin cinikayya da na bada hidima, wadanda za a bi wajen warware sabani tsakanin kasashe mambobi da suka amince da yarjejeniyar, kamar dai yadda taron watan Maris na birnin Kigalin kasar Rwanda ya amince da hakan.

Yanzu haka dai daukacin mambobin majalissar 60 sun amince da wannan kuduri, wanda kuma za a mika ga majalissar dattawan kasar domin neman amincewar ta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China