in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Afirka ta kudu ta amince da sharuddan gudanar da bincike game da iyalan Gupta
2018-04-25 11:20:54 cri

Kwamitin dake lura da harkokin cikin gida na kasar Afirka ta kudu, wanda aka dorawa alhakin bincikar matsayin kasancewa 'yan kasa, ga iyalan nan mawadata na gidan Gupta, ya amince da wasu sharrudda na gudanar da aikin sa.

An dai bude binciken ne, biyowa bayan umarnin da shugabar kwamitocin majalissar dokokin kasar Cedric Frolick ta bayar, game da alakar iyanan na Gupta da ma'aikatu daban daban na kasar. Da kuma yadda suka samu matsayin kasancewa 'yan Afirka ta kudu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China