in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta wallafa rahoto game da yanayin kare hakkin bil-Adama na Amurka
2018-04-24 20:14:07 cri
A yau ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wani rahoto game da yanayin kare hakkin bil Adama na kasar Amurka.

Rahoton mai taken "Bayanan kare hakkin bil-Adama na Amurka a shekarar 2017" ya mayar da martani ne kan rahotannin da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka ta fitar ranar 20 ga watan Afrilu game da batun kare hakkin bil-Adama na kasar Sin a shekarar 2017.

Baya ga wannan rahoto ofishin watsa labaran ya kuma fitar da bayanai game da yadda Amurka ta take hakkin bil-Adama a shekarar 2017.

Rahoton na kasar Sin ya kuma bayyana cewa, Amurka ta sake mayar da kanta a matsayin jagorar kare hakkin bil-Adama kana mai yanke hukunci kan wannan batu yayin da nata bayanan game da kare hakkin bil-Adama ke cike da nakasu.

Rahoton ya kuma zargi kasar Amurka da take hakkin bil-Adama, da nuna wariya, tarin kura-kurai a tsarinta na demokiradiya, wagegen gibi tsakanin talaka da mai hali, nuna wariya da cin zarafin wasu kungiyoyi kamar mata da kananan yara da matune masu nakasa da ma yadda take ci gaba da take hakkin bil-Adama a sauran kasashe na duniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China