in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar hukumar WHO ta jinjinawa kasar Ghana
2018-04-24 13:28:49 cri
Darakta mai kula da nahiyar Afirka na hukumar lafiya ta duniya WHO, Madam Matshidiso Moeti, ta yi jinjina ga shugabannin kasar Ghana, a jiya Litinin, bisa kokarinsu na inganta harkokin kiwon lafiyar jama'ar kasar ta hanyar tsarin UHC, wato tsarin kula da lafiyar daukacin al'ummar kasar.

Madam Moeti ta bayyana haka ne yayin ba da jawabinta, a taron koli na kula da lafiyar al'umma na shekarar 2018, wanda ke gudanar a birnin Accra, fadar mulkin kasar Ghana. Jami'ar ta ce ta yi mamaki ganin yadda ma'aikatar lafiyar kasar Ghana, da bangarori na masu kula da aikin jinya na kasar, suke samun babban ci gaba a fannin kula da lafiyar al'umma. Ta ce taron da aka gudanar wani dandali ne mai kyau, inda mutane za su hadu don tattauna ci gaba da sakamakon da aka samu, da kalubalolin da ake fuskanta.

Taron na yini 5, ya samu halartar kwararru a fannin ilimin lafiya, da manyan jami'ai, da masu zuba jari a fannin neman ci gaban al'umma, don tabbatar da cewa kasar Ghana ta samu biyan bukatar ta ta hanyar hadin gwiwa da wasu, da koyon fasahohin sauran kasashen dake nahiyar Afirka, ta yadda za ta cimma burinta na kula da lafiyar daukacin al'ummarta.

A nasa bangare, mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya ce kasar na neman daukar wasu sabbin matakai, don ba da tallafin jini, da sauran magunguna zuwa wasu wuraren da ke da nisa, ta yadda za a kyautata aikin biyan bukatun al'umma a fannin kiwon lafiya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China