in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan Libya sun tsamo gawawwakin mutane 11 daga tekun kasar
2018-04-23 13:56:31 cri

Rundunar sojojin ruwan kasar Libya, ta ce ma'aikatan ta masu sintiri a sassan tekun kasar, sun tsamo gawawwakin mutane 11, tare da ceto karin mutane 283 da ran su, bayan da jirgin roba da suke ciki ya nutse a wani wuri mai nisan kilomita 8 daga gabar Sabratha.

Kakakin rundunar Ayob Qassem ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin 'yan ci rani ne daga sassan nahiyar Afirka, tuni kuma aka kai su garin Al-Zawiya, mai nisan kilomita 45 yamma da birnin Tripoli.

Mr. Qassem ya ce, wasu ma'aikatan na daban, sun ceto karin wasu 'yan ci ranin 200, ciki hadda yara kanana 38, daga gabar tekun garin Zliten mai nisan kilomita 150 daga gabashin birnin Tripoli.

Libya dai na fuskantar kalubalen tsaro, da kwararar 'yan ci rani, tun bayan kifewar gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011, lamarin da ya sanya masu son shiga Turai ta tekun Mediteraniya ke tururuwar shiga kasar a kan hanyar su ta shiga Turai.

Alkaluman kididdiga sun tabbatar da cewa, sama da 'yan ci rani 4,000 ne aka ceto daga yankunan tekun kasar ta Libya cikin watanni 3 kacal na shekarar nan ta 2018.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China