in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fim din Scary Mother ya samu lambar karramawa a wurin bikin nuna fina-finan duniya na Beijing
2018-04-23 13:45:15 cri

A jiya Lahadi ne aka rufe kasaitaccen bikin nuna fina-finai na duniya karo na takwas da ya shafe tsawon mako guda a nan birnin Beijing, wato Beijing International Film Festival a turance, inda wani fim mai suna Scary Mother da kasashen Georgia da Estonia suka shirya tare, ya samu babbar lambar karramawa ta Tiantan ta fim din da ya fi fice.

Lambar karramawa ta Tiantan Award ta bikin nuna fina-finai na duniya karo na takwas wanda aka yi a birnin Beijing, ta samu takarar fina-finai 659 daga kasashen da yankuna 71 na fadin duniya, inda fina-finai 15 suka shiga zagayen karshe, ciki har da fina-finan kasashen waje 13, gami da na kasar Sin guda biyu. Wani fim da ake kira Operation Red Sea da kasar Sin ta dauka, ita ma ta samu lambar yabo. Mai tsara fim din, Yu Dong, ya gabatar da jawabin dake cewa, yana fatan sana'ar yin fina-finai ta kasar Sin za ta samu ingantuwa:

"A ganina mun sha wahala sosai wajen daukar wannan fim, haka kuma muna farin-cikin shiga takara ta lambar karramawa ta Tiantan Award. Muna matukar fatan ta hanyar halartar wannan biki, masu yin fina-finai daga fadin duniya za su ganewa idonsu yadda takwarorinsu na kasar Sin ke kokarin yin fina-finainsu, da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin inganta fasahar shirya fina-finai."

A nasa bangaren, shugaban kwamitin alkalan bayar da lambar yabo ta Tiantan a wannan karo, wanda kuma shahararren darektan fina-finai ne daga yankin Hongkong na kasar Sin, Karwai Wong, cewa yayi, lambar yabo ta Tiantan a wannan karo, na maida hankali sosai kan fina-fina masu taken mata. Wong ya ce:

"Daga cikin fina-finan 15, akwai guda biyar wadanda ke bayyana karfin mata, kuma mata ne zalla suka kasance darektocinsu. Wannan abu ya burge mu alkalai sosai, inda mu ke fatan mutane za su kara maida hankali kan hakkokin mata. Muna kuma fatan kara samun mata da za su shigo cikin sana'ar fina-finai don bayyana labaransu."

Kamar yadda darekta Wong ya ce, karfin mata ya bayyana sosai a wajen bikin bayar da lambar yabon. Wata tauraruwar fim daga kasar Iran, Mina Sadati, ta samu lambar yabo saboda kwazon da ta nuna a cikin wani fim mai suna Searing Summer. A cikin jawabin da ta yi, ta bayyana cewa:

"Ina matukar godiya saboda amincewa gami da yabon da na samu daga kwamitin alkalan fim, ina kuma matukar godiya ga kungiyar tsara fim din Searing Summer, musamman ma wanda ya bada umurnin fim din. Babu tantama, wannan lambar karramawar da aka ba ni, za ta ba ni kwarin-gwiwar ci gaba da kokarina wajen yin fina-finai. Saboda sana'ar fim da nake gudanarwa, na samu damar ziyartar kasar Sin har sau biyu, lamarin da ya sa nake kara sha'awar kasar. Ina fatan zan rika samun damar zuwa kasar Sin don kara fahimtar al'adunta. A karshe, ina so in ce, wannan lambar yabon da na samu, ba nawa ne ni kadai ba, har ma da sauran matan duniya, ciki har da matan kasar Iran, wadanda su ne suka nuna min cewa, ya kamata in yi iyakacin kokarina wajen aiki ba tare da na ja-da-baya ba. Ina so in mika wannan lambar karramawa ga daukacin mata gami da iyaye mata na kasata Iran."

Shi ma wani fim na daban mai taken mata, wato Scary Mother da kasashen Georgia da Estonia suka shirya cikin hadin-gwiwa, ya samu babbar lambar karramawa ta fim mafi fice, wato Best Feature Film a turance.

Wannan fim ya bayyana labarin wata mace wadda ta yi zabi tsakanin zaman gida ba tare da fita aiki ba, da sana'ar rubuce-rubuce, wanda ya nuna zaman rayuwar mata gami da ayyukansu, da irin karfi da jaruntakar da suka nuna.

Sauran wasu fina-finan da suka samu lambobin yabo na Tiantan sun hada da, fim din Journey's End daga kasar Birtaniya, da fim din The Testament da kasashen Isra'ila da Austria suka dauka tare, da kuma fim din Dede da kasashen Georgia da Qatar da Ireland da Holland da kuma Croatia suka shirya cikin hadin-gwiwa.

Kasaitaccen bikin nuna fina-finai na kasa da kasa karo na takwas wanda aka yi a nan birnin Beijing ya samu dimbin nasarori, inda aka shirya bukukuwa da dama, da nune-nunen kyawawan fina-finai na gida da na waje guda dari biyar, wadanda suka samu masu kallo sama da dubu dari biyu. Ban da wannan kuma, akwai kamfanoni 79 wadanda suka rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da suka shafi ayyuka 38 na sana'ar fina-finai, wadanda jimillar kudinsu ta zarce kudin Sin Yuan biliyan 26, abun da ya kafa sabon tarihi.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China