in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka rasu sakamakon harin kunar bakin wake na Kabul ya kai 52
2018-04-23 11:14:15 cri

Yawan mutanen da suka rasu, sakamakon harin kunar bakin wake na birnin Kabul, fadar mulkin kasar Afganistan ya karu zuwa 52, yayin da kuma wasu 112 suka ji raunuka.

Da yake bayyana hakan a shafin tweeter, kakakin ma'aikatar lafiyar kasar Waheed Majroh, ya ce bam din da aka dasa ya tashi ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, cikin dandazon mutane dake bin layin yin rajistar masu zabe a harabar wata makaranta. Cikin wadanda Bam din ya hallaka dai hadda mata 21, da yara kanana 5, yayin da wasu kuma suka samu raunuka masu tsanani.

Hukumar zaben kasar Afganistan ta tsaida ranar 20 ga watan Oktoba mai zuwa, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben 'yan majalissa da na shugabannin kananan hukumomi, a zaben da aka sha dage shi cikin shekarun da suka gabata.

An fara rajistar masu kada kuri'un ne tun daga ranar 14 ga watan Afirilun nan. Ana kuma sa ran zabar 'yan majalissun wakilai 249, domin gudanar da wakilci na wa'adin shekaru 5, baya ga sauran shugabannin kananan hukumomi da za a zaba.

Shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani, da babban jami'in gwamnatin kasar Abdullah Abdullah, da tawagar MDD, sun yi matukar Allah wadai da wannan hari, wanda tuni kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China