in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria: Hare hare ta sama sun hallaka mayakan IS 36
2018-04-23 10:40:36 cri

Rundunar sojin sama ta kasar Iraqi, ta ce ta hallaka mayakan kungiyar IS 36 a wani yanki dake kan iyakar kasar da Syria.

Wata sanarwa da rundunar hadin gwiwa ta JOC ta fitar, ta ce bayan samun wasu bayanan sirri, rundunar ta kai hari ta sama da jiragen yakin kasar Iraqi samfurin F-16, a wasu wurare da mayakan na IS ke samun mafaka, ciki hadda wani wuri da kusoshin kungiyar ke gudanar da ganawar sirri.

Kakakin rundunar JOC Yahya Abdul-Rasoul, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, harin na ranar Alhamis ya hallaka wasu shugabannin kungiyar ta IS su 5, baya ga wasu 6 da suka ji raunuka.

Firaministan kasar ta Iraqi Haider al-Abadi ne dai ya ba da umarnin kaddamar da harin na ranar Alhamis, a wani mataki na samar da kariya ga dakarun sojin Iraqi dake yammakin kasar, daura da iyakar Syria.

A ranar 9 ga watan Disambar bara ne dai Mr. Abadi, ya ayyana 'yantar da daukacin yankunan kasar Iraqi daga ikon mayakan IS, wadanda kafin lokacin ke iko da wasu muhimman yankunan kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China