in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Syria na kara dannawa yankunan kudancin Damascus
2018-04-23 09:51:08 cri

Rahotannin baya bayan nan na cewa, dakarun sojin kasar Syria na kara kutsawa yankunan kudancin birnin Damascus, a kokarin da suke yi na kakkabe gyauron mayakan kungiyar IS daga yankin.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SANA ya bayyana cewa, tuni dakarun sojin kasa suka yiwa yankin Hajar al-Aswad dake kudancin birnin tsinke, inda kuma suka amshe iko da wajen yankin.

Gabanin hakan mayakan kungiyar IS dake Hajar al-Aswad, sun sha ruwan bama bamai ta sama daga jiragen yakin gwamnati a daren ranar Lahadi. Sai dai duk da hakan, hukumar dake lura da kare hakkokin bil Adama ta Syria ta ce, mayakan na IS sun ki ficewa daga yankin, saboda tsoron gamuwa da karin hare hare ta sama daga jiragen yakin kasar Rasha muddin suka fita sararin Hamada.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China