Wata takardar bayani da kwamitin kolin ya fitar a Juma'ar nan ta bayyana cewa, yankin na Xiongan zai kasance wani wuri mai "matukar daraja a mataki na kasa da kasa", inda zai bi bayan yankin musamman na raya tattalin arziki na Shenzhen, da sabon yankin musamman na Shanghai Pudong.
A watan Afrilun shekarar bara ne dai Sin ta bayyana kafuwar yankin na Xiongan, wanda zai hade gundumomi guda uku dake lardin Hebei, mai nisan kilomita 100 daga kudu maso yammacin birnin Beijing.