in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jaddada niyyarta ta kare hakkokin jama'arta
2018-04-20 13:06:45 cri



Mai magana da yawun ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, Gao Feng, ya bayyana cewa, a halin yanzu, Sin da Amurka ba su yi shawarwari a hukumance ba, kan rahoton binciken sashe na 301 da Amurka ta yi, gami da jerin hajojin Sin da Amurka ta sanyama haraji. Gao ya kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin na tsayawa haikan kan kare muradun kasa da hakkokin jama'arta.

A kwanakin baya ne, ma'aikatar kasuwancin Amurka ta sanar da matakin haramtawa kamfanoninta sayar da hajoji da kayayyaki ga kamfanin sadarwar kasar Sin na ZTE har na tsawon shekaru bakwai. Ma'aikatar kasuwancin Sin ta mayar da martani kan wannan haramci, inda mai magana da yawunta Gao Feng ya sake jaddada cewa, kasar Sin na maida hankali sosai kan wannan al'amari, kana, a shirye take wajen daukar duk wani matakin da ya wajaba don kare halaltaccen hakki na kamfanin kasar. Mista Gao ya ce:

"Kar Amurka ta bijirewa niyyar gwamnatin kasar Sin. Idan Amurka tana son jawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin ta hanyar ba da kariya ga harkokin cinikayya ko kuma yin illa ga moriyar kamfanonin kasashen biyu, ta yi kuskure babba. Gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare muradun kasa gami da babbar moriyar al'ummarta, kuma sam ba za ta ja da baya ba."

A wani labarin kuma, an ce, Amurka za ta haramtawa kamfanin kasar Sin na Alibaba habaka harkokinsa a kasar, ko kuma hana kamfanin ci gaba da fadada ayyukansa a kasuwannin Amurka, har zuwa lokacin da gwamnatin kasar Sin ta soke tukunkumin da take sanyawa kamfanonin Amurka. Game da hakan, Mista Gao Feng ya bayyana cewa:

"Abun da Amurka ta yi, ya haifar da matsala ga yanayin gudanar da cinikayya da zuba jari a kasar. Amurka na daukar matakai ne kan kasar Sin, amma a karshe ita ma za ta sha wahala, saboda za ta rasa miliyoyin guraben ayyukan yi, sannan dubun-dubatar kamfanoninta za su fuskanci matsala. Har wa yau, hakan zai sanyaya gwiwar kasashen duniya wajen gudanar da cinikayya da zuba jari a kasar. Saboda abun da ka shuka, shi za ka girba."

A shekaran jiya wato ranar 18 ga wata, ma'aikatar kasuwancin Amurka ta sanar da cewa, za ta fara gudanar da bincike kan haramta jibge kayan karafa kirar kasar Sin da farashinsu ya yi kasa da yadda ya kamata. Game da haka, Gao Feng ya ce, tallafawa wasu sana'o'i fiye da kima ba zai tabbatar da samun dauwamammen ci gaban sana'o'in ba, inda ya ce:

"Bisa kididdigar da Amurka ta yi, daga cikin matakan da take aiwatarwa yanzu, na tallafawa harkokin cinikayyarta, akwai guda 223 wadanda suka jibanci kayayyakin karafa, abun da ya zarce kashi hamsin bisa dari na dukkan matakanta na tallafawa harkokin cinikayya. Ba ma son ganin wata kasa tana wuce gona da iri wajen amfani da matakan tallafawa harkokin cinikayya na hukumar WTO, haka kuma muna kin amincewa da yin amfani da matakan tallafawa harkokin cinikayya wajen ba da kariya ga harkokin ciniki. Tallafawa wasu sana'o'i fiye da kima ba zai tabbatar da samun dauwamammen ci gabansu ba. Don haka muna kira ga Amurka da ta dawo turba madaidaiciya wajen gudanar da harkokin ciniki irin na samun moriyar juna, da ba da taimako ga bunkasar harkokin cinikayya na fadin duniya, ta yadda sana'o'in cikin gidanta za su samu habaka yadda ya kamata."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China