in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministan Habasha ya kafa majalisar ministoci tare da bukatar su da yin aiki bisa gaskiya
2018-04-20 11:03:49 cri

A jiya Alhamis sabon firaiministan kasar Habasha, Abiy Ahmed, ya gabatar da sunayen mutanen da zai nada a majalisar ministocinsa da shugabannin da za su ja ragamar hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayyar kasar.

Ahmed, wanda ya gabatar da sunayen mutane 16 a matsayin mambobin sabuwar majalisar ministocin, inda ya gabatarwa majalisar dokokin kasar don neman amincewarta, kana ya nada mutane 9 a matsayin jami'an da za su shugabanci ma'aikatun gwamnatin tarayyar kasar.

Bayan amincewa da sunayen sabuwar majalisar kasar mai mutane 16, wanda Ahmed ya gabatarwa majalisar dokokin kasar don neman amincewarta, a halin yanzu firaiministan na Habasha yana da mambobi kimanin 29 a majalisar zartarwar kasar, daga cikinsu, 16 an riga an amince da ba su mukaman tun a jiya Alhamis, bayan da majalisar dokokin ta amince da bukatar.

Da yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar, Ahmed ya ce, babban aikin dake gaban sabuwar majalisar ministocin kasar, sun hada da yaki da rashawa, kafa tsarin shugabanci na gari, da kuma daukar matakan rage almubazzaranci da kudaden gwamnati.

Firaiministan ya kara da cewa, daya daga cikin manyan dalilan da suka sanya yin garambawul a tsarin majalisar zartaswar kasar shi ne, saboda yadda al'ummar kasar suka yi ta nuna rashin gamsuwarsu da yadda ake gudanar da mulkin rashin gaskiya da adalci a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China