in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya yi hasashen karuwar tattalin arzikin Afrika da kashi 3.1 a 2018
2018-04-20 09:56:24 cri

Bankin duniya ya yi hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afrika da kashi 3.1 bisa 100 a wannan shekarar ta 2018 sakamakon farfadowar da suke samu bayan da suka fuskanci koma baya cikin shekaru ukun da suka gabata a sanadiyyar faduwar farashin kayayyaki a kasuwannin duniya.

A cikin wani rahoton hasashe da bankin ya fitar game da tattalin arzikin Afrika, wanda ya saba wallafawa sau biyu a shekara a ranar Laraba, ya yi hasashen za'a samu bunkasuwar tattalin arzikin na Afrika da kashi 3.6 bisa 100 a shekarar 2019, da kuma kashi 3.7 bisa 100 a shekarar 2020.

Ana sa ran wannan hasashe zai kara janyo hankalin masu zuba jarin kasashen waje a nahiyar, da suka hada da kasashe masu tasowa kamar kasar Sin, da wasu kasashen duniya da suka ci gaba ta fuskar karfin tattalin arziki, lamarin da ake ganin zai kara yawan hada hadar cinikayya a kasashen Afirka, kamar yadda rahoton ya nuna.

Kasar Sin ta kasance kasa mafi yawan zuba jari a nahiyar Afrika, a hannu guda kuma, ita ce kasar da ta fi samar da kudaden gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a nahiyar ta Afrika.

Bankin duniyar ya ce, an yi hasashen ne bisa hasashen farashin albarkatun mai da karafu zai ci gaba da zama cikin kyakkyawan yanayi, za'a ci gaba da samun habakar ciniki a duniya, kuma za'a ci gaba da samun tallafi a kasuwannin hada hadar kudi na kasashen waje.

A wani taron manema labarai wanda aka watsa a kasashe 15, wanda ya gudana a ranar Laraba, Albert Zeufack, jami'in bankin duniya dake kula da sha'anin tattalin arzikin kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika ya ce, yana fatar gwamnatocin kasashen za su ci gaba da aiwatar da sauye sauye domin shawo kan matsalar rashin daidaito a tsarin tattalin arziki da bukasuwa harkokin zuba jari.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China