in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar OPCW ta tura tawagar jami'anta garin Duma na kasar Siriya
2018-04-19 12:51:39 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta ce, tawagar kungiyar haramta amfani da makamai masu guba ta duniya ko kuma OPCW a takaice, ta riga ta tura wani rukuninta zuwa garin Duma na yankin gabashin Ghouta dake karkarar birnin Damascus, da zummar binciken yanayin tsaron da ake cikin a wurin, don share-fagen zuwan kwararru a fannin makamai masu guba wurin a nan gaba.

Mataimakin ministan harkokin wajen Siriya, Faisal Mekdad, ya ce, gwamnatin kasar na da niyyar hada kai da kungiyar OPCW, da samar da duk wani saukin da take bukata wajen aiki. Babban darektan kungiyar OPCW, Ahmet Ümzücü, cewa ya yi, ya zuwa ranar 14 ga wata, dukkanin membobi guda tara na tawagar kungiyar sun rigaya sun isa birnin Damascus.

Gwamnatin Siriya ta kuma bayyana cewa, shedun gani da ido su 22 za su tafi Damascus don amsa tambayoyin tawagar kungiyar OPCW. Haka kuma, kungiyar na fatan membobin tawagarta zasu shiga cikin garin Duma ba tare da wani jinkiri ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China