in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya bukaci a samar da tsarin daidaita matsalar bashi a kasar Ghana
2018-04-19 12:47:29 cri
Bankin duniya ya bukaci kasar Ghana da ta dauki kwararan matakan da za su sassauta matsalar dunbun bashin da ya yiwa kasar katutu.

Albert Zeufack, babban masanin tattalin arziki mai kula da shiyyar Afrika ya bayyana a yayin wani taron bayar da Africa's Pulse, wanda ya shafi batun tattalin arzikin Afrika, yace, ya kamata kasar Ghana ta dauki kwararan matakan inganta kudaden shigarta na cikin gida, kuma ta dauki matakan kashe kudadenta bisa ka'ida kada su zarta adadin da ake son kashewa wajen gudanar da ayyukan raya kasa don daidaita matsalar dunbun bashin dake wuyan kasar.

Yayin da kasar ke da basuka da ya kai kashi 69.8 bisa 100 bisa yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa (GDP), kasar ta yammacin Afrika mafi samar da cocoa, zinare da man fetur a kasuwannin duniya, tana daya daga cikin jerin kasashen Afrika 18 wadanda aka bada rahoton suna fuskantar barazanar dunbun basuka.

Masanin tattalin arzikin ya ce "hakikanin abin da ke haifarwa kasashen matsalar basukan shi ne, kasashen sun soma mayar da hankali ne wajen zuwa kasuwannin duniya don ciyo bashi. Kasashen sun samar da takardun bashin Turai; kasashen sun karbi rance daga asusun waje don haka gwamnatocinsu suke ta kara yawan basuka na cikin gida wannan shi ne ainihin abin da ke faruwa a zahiri." (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China