in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin baje kolin shigi da fice na Guangzhou ya kasance wani muhimmin dandalin bunkasa cinikayya tsakanin Sin da Afirka
2018-04-19 13:33:00 cri



A ranar 15 ga wata, aka kaddamar da bikin baje kolin shigi da fice na kasar Sin karo na 123 a birnin Guangzhou. Wannan biki wanda ya kasance tamkar wata hanya ko alamar dake bayyana yadda kasar Sin take tsayawa wajen aiwatar da babbar manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga ketare cikin shekaru 61 da suka gabata, ya kuma kasance kamar wani muhimmin dandali ne na bunkasa cinikayya tsakanin Sin da Afirka. Bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kasar Sin ta kaddamar da babbar manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga ketare, kuma shekara ce ta cika shekaru 5 da gabatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Sakamakon haka, wannan bikin da ake shiryawa a Guangzhou yana da ma'anar musamman.

Mr. Xu Bing, mai magana da yawun bikin baje kolin shigi da fice na Guangzhou, kana mataimakin direktan cibiyar kula da harkokin cinikin waje ta kasar Sin ya gayawa wakilinmu cewa, a 'yan shekarun bayan nan, a lokacin da ake kokarin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", kamfanoni da masu sayayya wadanda suka fito daga kasashen Afirka suna ta karuwa, har ma suna da muhimmanci sosai ga bikin. Mr. Xu Bing ya bayyana cewa, "Bikin baje koli na Guangzhou ya dade yana kasancewa wani muhimmin dandalin bunkasa cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka. Yawan masu sayayya na kasashen Afirka ya kai kashi 5 cikin dari bisa jimillar baki masu sayayya wadanda suka halarci bikin. Saboda haka, sun kasance muhimman masu sayayya ne gare mu. Ina da imani cewa, a lokacin da tattalin arzikin kasashen Afirka ke samun saurin bunkasuwa, sannan ingancin kayayyakin kasar Sin ma na samun ingantuwa, yawan masu sayayya daga Afirka zai cigaba da karuwa, har ma yawan kamfanonin kasashen Afirka da za su halarci wannan bikin sayar da kayayyakinsu zai karu cikin sauri. Tabbas ne bikin baje koli na Guangzhou zai bayar da sabuwar gudummawa ga kokarin bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka."

A lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Guangzhou, Mr. Mbelwa Kairuki, jakadan kasar Tanzaniya dake nan kasar Sin ya ce, ya gamsu da kyakkyawan yanayin da bikin baje kolin Guangzhou ya samarwa masu sayayya da kamfanoni masu samar da kayayyaki, a waje daya, wannan biki ya zama wani muhimmin dandalin karawa juna sani tsakanin 'yan kasuwa na Tanzania. Mr. Mbelwa Kairuki ya bayyana cewa, "Bikin baje koli na Guangzhou ya kasance kamar wani babban aji, inda ba za a iya bude ido kawai ba, har ma za a iya koyon fasahar zamani. Abu mafi muhimmanci shi ne, za a iya samun ragi na kudin sayen kayayyakin saboda a wajen bikin, muna da damar yin mu'amala da wadanda suke kera kayayyaki maimakon sauran 'yan kasuwa. Bugu da kari, dukkan kamfanonin dake nune-nunen kayayyakinsu a bikin sun riga sun yi rajista a hukumar gwamnati, hakan zai sa mu amince da su. Saboda haka, ina fatan 'yan kasuwar Tanzania za su kalla da kuma su koyi karin abubuwa a gun bikin."

An fara kaddamar da bikin baje koli na Guangzhou ne a watan Afrilu na shekarar 1957, ya zama wani muhimmin dandalin yin mu'amala tsakanin Sin da sauran yankunan duniya. Mr. Lin Yijun, babban direktan wani kamfanin samar da kayayyakin wutar lantarki na kasar Sin ya gayawa wakilinmu cewa, kamfaninsa ya riga ya kwashe shekaru fiye da 10 yana yin cinikayya da kasashen Afirka. Wannan bikin baje kolin Guangzhou wani kyakkyawan dandali ne ga kamfaninsa da masu sayayya daga Afirka. A lokacin da ake bunkasa cinikayya tsakanin kamfaninsa da 'yan kasuwa na Afirka, ingancin kayayyakin kamfaninsa ma ya samu ingantuwa. Mr. Lin Yijun yana mai cewa, "Mun yi shekaru 10 ko fiye muna yin ciniki a kasashen Afirka 18. Yanzu yawan kayayyakinmu da muke sayarwa a yankin gabashin Afirka ya fi yawa. Bikin baje koli na Guangzhou wani muhimmin dandali ne na yin tattaunawa tsakaninmu da masu sayayya. A kullum masu sayayya suna mayar mana bayanan da suka samu game da ingancin kayayyaki, sannan mu kan kyautata inganci ko amfanin kayanmu."

Mr. Anieke Benjamin Cheibuzor, wani dan kasuwa daga Najeriya yana farin ciki sosai saboda ya samu kayayyaki masu inganci kuma masu rahusa a gun bikin. Anieke Benjamin ya ce, "Da farko dai ina son sayen wasu na'urorin sa ido ne. Saboda haka, ina bukatar neman samun kamfanoni wadanda suke kera irin wadannan na'urorin sa ido. Abin farin ciki shi ne, a gun bikin, na samu irin wadannan na'urorin sa ido masu inganci, kuma masu rahusa sosai kai tsaye. Yanzu ina son sayen wasu batura masu aiki da hasken rana da wasu na'urorin sadarwa da ake amfani da su a kasarmu Najeriya. Lalle na samu damar koyon fasahar yin amfani da su a gun bikin."

Mr. Xu Bing, mataimakin direktan cibiyar kula da harkokin cinikin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, bisa shirin bunkasa Intanet Plus da kara yin amfani da Big Data na kasar Sin, cibiyarsa ta tsara wani shirin sauyawa da kuma kyautata salon bikin baje koli na Guangzhou. Bisa sabon shirin, wannan bikin baje koli na Guangzhou zai zama wani dandalin yin cinikayya a ko da yaushe a duk shekara. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China