in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta baiwa Gambiya guraben karo karatu 400 na gajeren zango
2018-04-19 09:54:03 cri

Gwamnatin kasar Sin ta baiwa gwamnatin kasar Gambiya guraben karo karatu 400 na gajeren zango a matsayin wani bangare na kyautata mu'amala a fannin ilmi a tsakanin kasashen biyu, ministan yada labaran kasar ta Gambiya, Demba A. Jawo shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a jiya Laraba.

Ya ce, gwamnatin kasar Sin ta bayar da wadannan guraben kwasa-kwasai na gajeren zango ne ta hanyar tallafawa shirin mu'amalar kasashen biyu. Kashin farko na 'yan kasar Gambiyan da za su halarci kwas din su 20, za su tashi zuwa kasar Sin tun da yammacin ranar Laraba.

Jawo ya ce, wadanda za su ci gajiyar shirin za su samu horo ne a fannin yada labarai da harkokin sadarwa wadanda ke aiki da kafafen yada labarai a kasar da kuma wasu jami'an gwamnatin kasar, kuma wadanda ke aiki a ma'aikatu da hukumonin yada labaran kasar ta Gambiya.

Ya kara da cewa, kaso na biyu ya kunshi mutane 25 ne, za su tashi zuwa kasar ta Sin a mako mai zuwa inda za su samu horo a fannin tsaron intanet.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China