in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Amurka da Korea ta arewa sun fara tattaunawa a matsayin koli
2018-04-18 14:04:53 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana a jiya Talata cewa, Amurka da Korea ta arewa, sun fara tattaunawa kai tsaye a matsayin koli.

Trump ya yi hira da manema labarai, bayan ya gana da firaministan kasar Japan Shinzo Abe wanda ya kai ziyara kasar, inda ya bayyana fatansa na ganawa da shugaban kasar Korea ta arewa Kim Jong Un. A cewarsa bangarorin biyu na mutunta juna, da girmama juna kwarai da gaske. Ban da wannan kuma, ya ce, Amurka na duba wurare 5 da za a gudanar da wannan ganawa, amma ban da kasar Amurka.

Haka zalika, a ran 9 ga wata, Trump ya shedawa manema labarai cewa, zai gana da Kim Jong Un a watan Mayu ko Yuni. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China