in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministar Birtaniya ta yi afuwa kan korar 'yan ci rani bakaken fata
2018-04-18 13:04:25 cri

A jiya Talata, firaiministar Birtaniya Theresa May ta yiwa kasashe 12 dake gabar tekun Caribbean afuwa kan kuskuren da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta yi na korar 'yan cin rani bakaken fata 'yan asalin kasashen tekun Caribbean.

Theresa May ta nuna cewa, wadannan 'yan ci rani da jikokinsu sun ba da gudunmawa sosai ga al'ummar Birtaniya, wadda gwamnati da jama'ar Birtaniyan ba za su iya mantawa ba.

An ba da labarin cewa, wasu bakaken fata da suka kaura zuwa Birtaniya daga Afrika tun suna yara, sun shafe rayuwarsu a kasar cikin dogon loakci, amma ba su sami matsayin takardun shaidar zama 'yan kasar Birtaniya ba har yanzu. Tun daga karshen watan jiya, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta yi gargadin korar yawancinsu, matakin da ya jawo hankalin wadannan kasashe 12, har ma da mambobin majalisar dokoki 140 sun nemi an sake daidaita wannan batu domin yin bincike yadda ya kamata kan daidaikun mutane.

An ce, Birtaniya tana da karancin karfin kwadago bayan yakin duniya na biyu, hakan ya sa ta goyi bayan bakaken fata daga gabar Caribbean da kuma yankuna dake karkashin jagorancin Birtaniyan da su kaura zuwa Birtaniya. Amma saboda karuwar yawan bakaken fata a Birtaniya, wasu 'yan Birtaniya sun rasa aikin yi, dalilin da ya haddasa suke gaba da juna kuma lamarin ya tsananta rikici a tsakanin al'umma. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China