in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a hada hannu wajen kawo karshen rikicin Libya
2018-04-18 10:06:05 cri

Tarayyar Afrika AU, ta yi kira da a hada hannu wajen daukar matakan warware rikicin kasar Libya, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a kasar dake arewacin Afrika.

Wannan na zuwa ne bayan wani taro karo na 5 da kwamitin manyan jami'an AU suka yi kan Libya, wanda ya gudana a Addis Ababa na Habasha, yayin da aka gaza samun ci gaba game da tsarin siyasar kasar da kuma rashin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa.

Tun daga shekarar 2011 Libya ta afka yakin basasa bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Muammar Gadhafi.

Rundunar kawance na Tarayyar Afrika da MDD da Tarayyar Turai, na kokarin taimakawa 'yan ci rani dake watangarari a kasar, tare da kokarin datse hanyoyin safarar bil adama da na kwararar 'yan ci rani.

Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat ya shaidawa taron cewa, yanayin da aka ciki a Libya na barazana ga kasar da al'ummarta da kuma kasashe dake makwabtaka da ita, wadanda rashin tsaron ya fi shafa, wanda kuma ya haifar da yanayin da Libya ke ciki a yau. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China