Mahukuntan kasar Sin sun bayyana aniyar aiwatar da wata sabuwar manufa, wadda za ta baiwa kamfanonin kasashen waje damar zuba jari a masana'antun kera nau'o'in motoci daban daban.
Wani babban jami'in hukumar tsara manufofin ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta Sin ne ya bayyana hakan a Talatar nan, yana mai cewa masu zuba jari na ketare, za su iya mallakar hannayen jari a fannin kera motoci na musamman, da wadanda ke amfani da makamashin da ake iya sabuntawa nan gaba cikin wannan shekara ta 2018.
Kaza lika za a samar da wannan dama ga masu zuba jari a fannin kirar motocin da daidaikun mutane ke saya daga shekarar 2020, da kuma motocin amfanin al'umma da yawa a shekarar 2022.(Saminu Alhassan)