Mai magana da yawun hukumar kididdiga ta kasar Sin, Xing Zhihong ya ce, daga watan Janairu zuwa Maris din bana, ayyukan gona na kasar Sin sun samu habaka sosai, kuma yawan naman dabbobin gida ciki har da naman saniya da rago da aka sarrafa ya zarce ton miliyan 23, wanda ya karu da kashi 1.8 bisa dari na makamancin lokacin a bara. Har wa yau, ayyukan masana'antu su ma sun bunkasa yadda ya kamata. A waje daya kuma, harkokin bada hidima na kasar Sin sun samu ci gaba cikin sauri, inda ma'aunin ayyukan kamfanonin bada hidima na kasar ya karu da kashi 8.1 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara.
Mista Xing ya ce, a takaice dai, daga watan farko zuwa na uku na bana, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasa ta hanyar da ta dace kuma yadda ya kamata, kana, ana kara samun wasu abubuwan da suka taimaka ga habakar tattalin arzikin kasar, abun da ya gina ingantaccen tubali ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a bana. (Murtala Zhang)