Mai magana da yawun ma'aikatar ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na bukatar kamfanoninta dake kasashen waje su bi dokokin kasashen da suke, da gudanar da cinikayya bisa doka. Kamfanin sadarwa na ZTE na hadin-gwiwa da kamfanonin Amurka sama da dari a fannonin da suka shafi zuba jari da cinikayya, da bayar da gudummawar dubun-dubatar guraben ayyukan yi a Amurka. Sin na fatan Amurka za ta daidaita wannan sabani bisa doka, tare da kokarin samarwa kamfanonin kasar Sin wani kyakkyawan yanayin kasuwanci cikin adalci kuma bisa doka da oda. (Murtala Zhang)