in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shugabannin dakarun Amurka da Afrika a Nijeriya
2018-04-17 09:14:32 cri

An bude taron dake da nufin bunkasa hadin gwiwa, tsakanin dakarun kasashen duniya, ta fuskar tunkarar kungiyoyin ta'addanci, wanda Amurka ke daukar nauyi a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Manyan jami'an soji daga a kalla kasashen Afrika 30 da shugabannin rundunonin soji daga Amurka da Turai ne suka halarci bikin bude taron karo na 6 mai taken "karfafa hadin gwiwa: yaki da kalubalen tsaro a Afrika".

Shugabannin sojin sun yi musayar bayanai kan barazanar dake fuskantar Afrika, inda suka bayyana Al-shabaab a matsayin ta yankin gabashin nahiyar da Boko Haram a yankin yammaci.

Yayin bude taron, babban hafsan sojin Nijeriya Abayomi Olonisakin, ya bukaci shugabannin rundunonin sojin Afrika, su samar tare da rungumar dabarar hadin kai wajen tunkarar barazanar tsaro mabambanta da nahiyar ke fuskanta.

Babban hafsan sojin ya kuma ce akwai bukatar kara koyon dabarun yaki ta hanyar samun horo da musayar bayanan sirri da samun makamai a tsakanin rundunonin soji, yana mai sa ran taron zai kara wa shugabnnin sojin nahiyar sabbin dabaru da hanyoyin magance dimbin kalubalen tsaro da aikin soji ke fuskanta. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China