Madam Hua ta fadi haka ne a yau Litinin, a wajen taron manema labaru da aka saba da yi. A cewarta, yadda kasashen 3 suke kai hari ga kasar Syria ya sabawa tanadin dokokin kasa da kasa, na haramta yin amfani da karfin soja, haka kuma matakin da suka dauka, ya sabawa babban kundin tsarin MDD.
Kakakin kasar Sin ta kara da cewa, jami'an kasashen 3 sun ce "mai yiwuwa ne" gwamnatin kasar Syria ta yi amfani da makamai masu guba, sa'an nan suna "kokarin neman shaidu". Duk da cewa ba a tabbatar da ainihin abun da ya faru ba tukuna, an dora laifi kan wata gwamnati, gami da kai mata hari kai tsaye. Hakan a ganin kasar Sin, ba wani mataki na daukar nauyi ba ne.
Jami'ar kasar Sin ta kara da cewa, kasar Sin na adawa da amfani da makamai masu guba, bisa ko wane irin dalili. Kuma ta bukaci a yi cikakken bincike kan batun makamai masu guba na kasar Syria, don gano ainihin abun da ya faru.(Bello Wang)