in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing
2018-04-16 14:33:10 cri

A jiya da dare ne aka bude bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing karo na takwas a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Bikin da ya zuwa yanzu, ya zama wata muhimmiyar alama ta ci gaban fina-finan duniya, da kuma dandalin musayar ra'ayoyi da kuma hadin gwiwa ga masu aikin fina-finai na duniya.

A jiya Lahadi da dare ne aka bude bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing karo na takwas, inda ya samu halartar shahararrun taurari da darektocin fina-finai da suka hada da Chloe Grace Moretz da ta fito daga Amurka da Chan Ho-San, wato Peter Chan daga yankin Hongkong na kasar Sin da Wu Jing da ya zo daga babban yankin kasar Sin da sauransu.

A wurin bikin, mataimakin shugaban kwamitin shirya bikin, Du Feijin ya bayyana cewa, tun bayan da aka kaddamar da bikin a shekarar 2010, har kullum bikin na dukufa kan hada karfin masu aikin fina-finai da bunkasa al'adun fina-finai, inda ya ce, "Fina-finai harshe ne na bai daya ga kasashen duniya. Baki kimanin dubu 15 da suka fito daga sassan fina-finai 300 na kasashe da sassan duniya sama da 50 sun halarci bikin, wadanda suka hadu a nan birnin Beijing, don yin shawarwari kan bunkasar fina-finai, matakin da tabbas zai kara ciyar da fina-finan duniya gaba."

A cikin 'yan shekarun baya, fina-finan kasar Sin sun shiga wani lokaci na saurin bunkasa. A shekarar 2017 da ta gabata, adadin kudin tikiti na fim mai taken Wolf Warriors II ya samu kaiwa wani matsayin da ba a taba samu ba bisa ga kudin tikiti da ya kai RMB yuan biliyan 5 da miliyan 680 da aka sayar. Baya ga haka, akwai mutane miliyan 159 da suka kalli fim din, abin da ya sanya shi zama zakara ta fannin fim din da ya fi samun masu kallo a kasuwar wata kasa. A farkon wannan shekara ta 2018 kuma, wasu fina-finai uku na kasar Sin da suka hada "Operation Red Sea" da "Detective Chinatown II", duk sun sayar da tikitin da kudinsu ya zarce RMB yuan biliyan 2.

Malam Chen Sicheng, wanda shi ne darektan fim din mai taken "Detective Chinatown II", ya bayyana imaninsa ga kasuwar fina-finai na kasar Sin nan da shekaru 10 masu zuwa, yana mai cewa, "Na gaskata cewa, nan da shekaru 10 masu zuwa, adadin kudin tikitin fina-finai na kasar Sin da za a samu zai kara habaka, sai dai ina fatan karin masu kallo na kasashen ketare za su samu damar kallon fina-finan kasar Sin. Kamar yadda kowa ya sani, yawan kudin tikitin da fina-finan Hollywood suke samu a sassan nahiyar Amurka ta arewa ya kai kaso 30 cikin dari zuwa kaso 40 cikin dari ne kawai na kudin da suke samu gaba daya, wato suna samun ragowar kudin ne daga sauran sassan duniya. Da zuciya daya nake fatan masu aikin fina-finai na zamaninmu za su yi kokari tare, don kara samar da fina-finai masu kyau ga duniya."

Mr. Wu Jing, darektan fim din nan Wolf Warriors II a nasa bangare ya ce, masu aikin fina-finai na kasar Sin za su ci gaba da samar da fina-finai masu kyau ga masu kallo na wannan zamani. Ya ce, "Mun shafe tsawon shekaru uku muna shiryawa tare da daukar wannan fim din, daga karshe mun kaddamar da wannan fim mai kunshe da hotuna 4077, yayin da masu kallonsa suka kai miliyan 159, adadin da ya shaida kokarin da mu masu aikin fina-finai ke yi da kuma amincewar da masu kallo na kasar Sin suka nuna wa fina-finan kasar. Don haka, a madadin dukkanin masu aikin fim, za mu rubanya kokarinmu, don kara samar da fina-finai masu inganci ga masu kallo."

Za a rufe bikin na wannan karo a ranar 22 ga wata. A yayin bikin, za a fid da fitattun fina-finan da za a ba su lambobin yabo na Tiantan, za kuma a nuna fina-finai masu kyau na kasar Sin da ma na sauran kasashen duniya, har wa yau, za a gudanar da taron tattaunawa tsakanin masu aikin fina-finai. A matsayin wani muhimmin bangare na bikin, akwai fina-finai 13 na kasashen duniya da suka shiga takarar neman lambar yabon na Tiantan, ciki har da "Barefoot" na kasar Czech da "Dark Wind" na kasar Indiya da "Dog" na Faransa. Baya ga haka, akwai fina-finai biyu na kasar Sin.

Za a kuma sanar da fina-finai 10 da za su samu yabon a yayin rufe bikin da za a shirya a ranar 22 ga wata. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China