in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 7
2018-04-15 15:44:46 cri

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe mayakan Boko Haram 7 a cigaba da aikin murkushe mayakan da kuma tarwatsa maboyarsu dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojojin kasar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa, dakarun sun samu nasarar hallaka mayakan 'yan ta'addan ne a lokacin da suka bude wuta kansu a lokuta daban daban a ranar Jumma'a.

Wasu daga cikin mayakan na Boko Haram an hallakasu ne a cikin dajin Sambisa, wajen da ya taba zama babban sansanin horas da mayakan 'yan ta'addan dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar, in ji Nwachukwu.

A cewar kakakin rundunar sojojin, a lokacin samamen sun yi nasarar damke wanda ke yiwa kungiyar ta Boko Haram leken asiri.

Wanda ake zargi da yiwa kungiyar leken asiri mai suna Modu Chari, dakarun sojojin sun kama shi ne a lokacin da yake yiwa kungiyar aikin tattara bayanan sirri.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China