Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a Hedkwatar AU dake birnin Addis Ababa na Habasha, Kwamishinan kwamitin sulhu na AU Isma'il Chergui da mataimakin Sakatare Janar na MDD kan ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, sun bayyana damuwa game da ci gaban rikici a yankunan PK5 dake makwabtaka da Bangui babban birnin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
Jami'an biyu, sun kai ziyarar yinin uku birnin Bangui, daga ranar 10 zuwa 12 ga wannan watan, inda suka tattauna da jami'an gwamnati da wakilan kungiyoyin al'umma da kungiyoyin mata da shugabannin addini da sauransu.
Sun kuma yi ta'aziyyar asarar rayuka da aka yi, ciki har da jami'an wanzar da zaman lafiya na kawance wato (MINUSCA), yayin wani samame da jami'an da hadin gwiwar jami'an tsaron kasar suka kai ranar 8 ga wata, a wani yunkuri na kawo karshen ayyukan bata garin dake barazana ga rayuwar al'umma a yankin Pk5 dake makwabtaka da Bangui,wadda kuma ita ce cibiyar tattalin arzikin birnin. (Fa'iza Mustapha)